2 Corinthians 5

1Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama. 2Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya. 3Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba.

4Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa. 5Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa.

6Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji. 7Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba. 8Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji.

9Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi. 10Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari’a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau.

11Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku. 12Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba.

13Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne. 14Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu. 15Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi.

16Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar’anta kowa bisa ga ma’aunin ‘yan’adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar’anta kowa ta haka. 17Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al’amura sun shude. Duba, sun zama sababbi.

18Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu. 19Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu.

20Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: ‘’ku sulhuntu ga Allah!‘’ Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.

21

Copyright information for HauULB